Gwamnatin tarayya ta sanar da kara karfafa hulda tsakaninta da kasar China dan horas da sijoji da kuma kera makamai.
Tace hakan hanyace da zata taimakawa kasar wajan yaki da ta’ddanci da sauran matsalolin tsaro.
Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa, ranar Alhamis bayan gawar da shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi da ministan harkokin waje na kasar China, Wang Yi.
Yusuf yace irin wannan hadaka da kasar China zata taimakawa Najeriya dama makwabtanta wajan samar da tsaro.