Masana tattalin Arziki sun bayyana cewa, nan da watan Disamba na shekarar 2025 farashin kayan masarufi zai sauka da kaso 27.1.
latest NESG-Stanbic IBTC Business Confidence Monitor ne suka fitar da wadannan bayanai inda suka ce wannan zai baiwa ‘yan kasuwa dama sauran jama’a kwarin gwiwa kan matsin tattalin arzikin da aka samu kai a ciki.
Hauhawar farashin kayayyaki da tashin farashin man fetur da karyewar darajar Naira ne kan gaba cikin abubuwan dake damun ‘yan Najeriya.