Pastor Korede Komaiya ya bayyana cewa, talauci alamace ta rashin tsoron Allah da yawan zunubi.
Faston ya bayyana hakane ga mabiyansa a cikin cocinsa.
Yace a rubuce yake cewa, wadanda suka bi Allah, zasu samu rayuwa ta jin dadi. Dan haka yace talauci alamace ta rashin tsoron Allah da yawan zunubi.
Bidiyon da yake wannan magana ya yadu sosai a kafafen sda zumunta inda akai ta masa raddi.
Yace yawanci ba’a sanin ainahin halin mutum sai idan ya samu kudi. Ya kara da cewa, yawanci talakawan da zaka ga suna kankan da kai, dama ce basu samu ba.