Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauka a kasar UAE inda ya je dan halartar taron ci gaban kasashe.
Fadar shugaban kasar ta sanar da cewa karamin ministan harkokin kasashen waje na kasar ta UAE Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan ne ya tarbi shugaba Tinubun.