Yayin da wutar lantarkin Najeriya ta zama marar tabbas, kamfanoni da ma’aikatu 250 ne suka daina amfani da wutar da gwamnatin Najeriya da kamfanonin rarraba wutar na Discos ke samarwa inda suka koma samarwa kansu wutar.
Mafi yawancin kamfanonin na amfani da wutar lantarkin sosai. Gashi Gas yayi tsafa, ga kudin wutar ana karba da yawa ga wutar ba tabbas shiyasa suka samarwa kansu mafita.
A shekarar 2021, tsohon shugaban kaa, Olusegun Obasanjo shima ya dana amfani da wutar lantarkin Najeriya inda ya koma samarwa kansa wutar a dakin karatunsa dake Abeokuta jihar Ogun.
Jimullar wutar da wadannan kamfanoni ke samarwa kansu ta kai karfin 6,500 megawatts wanda hakan ke nufin karfin wutar yafi wanda Gwamnatin Najeriya ke samarwa wadda ke da karfin 5,000MW a mafi akasari.
Gwamnati tuni ta yi doka inda ake baiwa kamfanoni lasisin samarwa kansu tashar wutar lantarki da zasu yi amfani da ita su kadai ba tare da sayarwa da kowa ba.
Babbar tashar wutar lantarkin da ake da ita a Najeriya itace ta Dangote wadda ke samar da wutar lantarkin me karfin 1,500MW.
Wasu daga cikin kamfanoni da ma’aikatun dake samarwa kansu wutar lantarki ba tare da dogaro da gwamnati ba sun hada da MTN Nigeria, the Nigerian National Petroleum Company Limited, Shell, Nigerian Breweries Plc, Flour Mills of Nigeria Plc, Mobil Producing Nigeria Unlimited, Kaduna refinery, Warri refinery, Lafarge Cement Wapco Nigeria Plc, Procter and Gamble Nigeria Limited, da Bank of Industry Ltd.
Sauran sune Seven-Up Bottling Company Plc, First Bank of Nigeria Plc, Dangote Cement Plc, Lekki Port LFTZ Enterprise Limited, Guinness Nigeria Plc, Chevron Nigeria Limited, Nestle Nigeria Plc, Total Upstream Nigeria Limited, Aluminium Smelter Company of Nigeria, De-United Foods Industries Limited, Sagamu Steel Nigeria Limited, British American Tobacco Nigeria Limited, Unilever Nigeria Plc, Total E & P Nigeria Limited, da Mikano International Limited.
Sauran sune Federal Airports Authority of Nigeria, Airtel Networks Limited, Nogap Power Development Company Limited, Shell Exploration & Production Company Limited, Esso Exploration & Production Nigeria Limited (Usan OML 138), Indorama Eleme Petrochemicals Limited, Cadbury Nigeria Plc, Honeywell Flour Mills, Atlantic International Limited Refinery & Petrochemical Limited, Julius Berger Nigeria Plc, Okamu Oil Palm Company, PZ Cusson Nig Plc.
Daga cikin jami’o’in dake samawa kansu wutar lantarki akwai su University of Lagos, Abubakar Tafawa Balewa University, Federal University Ndufu-Alike IKWO, Usmanu Danfodiyo University, Obafemi Awolowo University, Federal University of Petroleum Resources, Nnamdi Azikiwe University, Awka, Federal University of Agriculture, Makurdi, Bayero University, Kano, da University of Benin.
Akwai kuma University of Abuja, University of Calabar & Teaching Hospital, Cross River State, University of Agriculture Micheal Okpara, Umetuke, Abia State, University of Maiduguri & Teaching Hospital, Borno State, Federal University of Agriculture, Abeokuta Main Campus, Ogun State, da the Federal University Gashuwa, Yobe State.
Itama makarantar horas da sojojin Najariya, NDA ta samu lasisin samarwa kanta wutar lantarkin dan daina dogaro da wutar lantarkin Najeriya.
[…] A wani rahoto da hutudole ya kawo muku, kun ji cewa sama da kamfanoni da ma’aikatun gwamnati 200 ne suka daina amfani da wutar gwamnat… […]