Shahararren me shigar mata da daudanci a Najeriya wanda aka fi sani da Bobrisky ya yi magana bayan da shugaban kasar Amurka ya haramta luwadi da Madigo.
Bobrisky yayi suna sosai wajan daudanci inda har a karshe yace ya bar Najeriya da zama saboda takurawar da aka masa.
A ranar da aka rantsar dashi a matsayin shugaban kasar Amurka a karo na 2, Donald Trump ya bayyana cewa, jinsin maza da mata kawai suka sani a Amurka.
A rubutun da yayi a shafinsa na sada zumunta, Bobrisky ya bayyana cewa, Ya ji ance shugaban Amurka, Donald Trump yace maza da mata kawai ya sani, amma shi gashi ya koma mace, yace idan ana so, zai bude aga hujja.