Shugaban kwamitin dake kula da yanda Gwamnatin tarayya ke kashe kudi, James Faleke ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ba zata iya ci gaba da biyan kudij tallafin wutar lantarki ba.
Ya bayyana hakane yayin da ma’aikatar kudi ke bayanin yanda zata kashe kudadenta a shekarar 2025.
Gwamnatin tarayya dai ta ware Naira biliyan 705 dan biyawa ‘yan Najeriya tallafin wutar a shekarar 2025.
Saidai Falake yace sam babu bukatar hakan musamman lura da yanda farashin wutar labtarkin ke ta kara tashi kullun da kuma yanda darajar Naira ke ci gaba da faduwa.