
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya soki tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda sukar Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.
A martanin da yawa El-Rufai ta shafin X, Shehu Sani yace rashin aikin yi da kuma damuwa da munafurcine suka dabaibaye El-Rufai.
Yace a lokacin yana gwamnan Karaduna, El-Rufai bai dauki ‘yan adawa a matsayin komai ba, amma wai yau shine yake nuna yana tare da ‘yan adawa.
Yace kawai dan ba’a bashi mukami a Gwamnatin Tinubu bane abin ke damunshi yake ta bi yana bata Gwamnatin.
A baya dai, El-Rufai ya bayyana cewa jahilaine a cikin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.
Shehu Sani ya kara da cewa a yanzu El-Rufai yana ta bine duk wani taron dattawa a Arewa yana yada manufar bangaranci da raba kai.