Tuesday, March 17
Shadow

A A Rano ya bude gidan mai na farko wanda babu me zuba man fetur wanda zai rika aiki ba dare ba rana

Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, me kamfanin A A Rano ya bude gidajen man fetur na farko da zasu rika aiki awanni 24, ba dare ba rana kuma babu me zuba mai.

Mutum ne da kansa zai shiga da abin hawansa gidan man ya sa katinsa na ATM ya biya ya kuma zuba man ya kara gaba.

A A Rano sun hada kai da kamfanin Petrosoft Limited ne dan samar da wannan tsari.

Ya bayyana cewa, hakan zai saukakawa Kwastomominsu shan man sannan kuma zai saukaka musu aiki suma.

A A Rano yace sabbin gidajen man zasu fara aiki a watan Janairu.

Karanta Wannan  Kotu Ta Yanke Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Tsawon Shekaru Uku Ga Baturen Zaben Da Ya Yi Magudi Har Ta Kai Ga Akpabio Ya Zama Sanata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *