Friday, July 17
Shadow

A dakin Otal Muka kama Nnamdi Kanu yana hutawa da wata mata>>Gwamnatin Tarayya

A ci gaba da shari’ar da ake tsakanin shugaban kungiyar dake son kafa kasar Biafra, IPOB, watau Nnamdi Kanu da gwamnatin tarayya, Gwamnatin tarayya ta gabatar da shaidarta na farko.

Lauyan Gwamnatin tarayya ya nemi shaidar ya rufe fuska saboda tsaro kuma Alkalin dake shari’ar ya amince da hakan hakana shima lauyan Nnamdi Kanu bai kalubalanci hakan ba.

Shaidar ya bayyana fuska a rufe inda yace shine ya jagoranci jami’an tsaro zuwa dakin da Nnamdi Kanu yake a Otal.

Ana zargin Nnamdi Kanu da cin amanar kasa, da aikata ayyukan ta’addanci.

Karanta Wannan  Nayi shaharar da ba zan taba yin taĺauci ba>>Inji Gfresh Al-amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *