Wednesday, January 15
Shadow

A farashin 898 muka sayi man fetur daga matatar man Dangote>>NNPCL

Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, a farashin Naira 898 suka sayi man fetur daga matatar man fetur ta Dangote.

A yau ne dai kamfanin na NNPCL suka fara daukar man fetur din daga matatar man ta Dangote bayan shan dambarwa tsakanin Gwamnati da matatar man.

Masu sharhi da yawa na ganin cewa, sayen man fetur din a wannan farashin daga matatar Dangote na nufin bata canja zani ba.

Inda wasu ke zargin cewa, Gwamnati ce ta yi kaka gida a lamarin shiyasa man yayi tsada haka.

A baya dai ana tsammanin matatar man fetur ta Dangote zata kawo saukin Man fetur a kasarnan amma hakan da kamar wuya.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Rundunar yan sandan Najeriya na neman wani bátưré ruwa a jallo bayan ta bakaɗo yana kitsa yadda za a yiwa Tinubu júyíɲ mulkí

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *