
Kasashen Canada,UK, Australia da New Zealand zasu kakabawa wasu jami’an Gwamnatin kasar Israela 2 takunkumi.
Wadanda za’a kakabawa wannan takunkumi sune Itamar Ben Gvir da Betzalel Smotrich wanda ‘yan siyasa ne masu rura wutar ci gaba da kisan Falasdiynawa.
Rahotanni a baya sun ce duka kasashe masu fada a ji na Duniya sun amince a dakatar da yakin Gaza in banda kasar Amurka.
Dubban mutane ciki hadda mata da kananan yara ne aka kashe a Gàzà wanda kasashen Duniya ke cewa an aikata laifukan yaki.