Friday, July 17
Shadow

Kwankwaso yaci amanarmu mun barwa APC shi, inji jam’iyyar NNPP

DA DUMI-DUMI: Kwankwaso yaci amanarmu mun barwa APC shi, inji jam’iyyar NNPP.

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa zai zama babban farin ciki a gare ta idan dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya koma jam’iyyar mai mulki ta APC.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Mista Oginni Olaposi, ya fitar ranar Lahadi a Legas.

Olaposi ya mayar da martani ne kan murabus din da Abdullahi Ganduje ya yi daga shugabancin APC da kuma jita-jitar cewa ya yi hakan ne domin ba wa Kwankwaso damar shiga jam’iyyar.

“Kwankwaso ya ci amanar da muka ba shi ta hanyar kokarin kwace jam’iyyar daga hannun wanda ya kafa ta, Dokta Boniface Aniebonam, wanda ya ba shi damar samun tikitin takarar shugaban kasa kyauta a 2023,” in ji shi.

Karanta Wannan  Ba zan tsaya takara a shekarar 2027 ba, na hakura haka, a samu wani matashi da bai kaini Shekaru ba shima ya zo ya gwada>>Inji Dan majalisar wakilai daga jihar Sokoto, Hon. Abdussamad Dasuki

~ Hikima Radio and TV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *