
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, Yunwa ta kamashi.
Amaechi ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwarsa.
Yace Dukkan mu nan muma cikin yunwa, idan baku ciki ni ina cikin yunwa.
Amaechi yace duk da yana APC amma bai zabi Tinubu ba a matsayin shugaban kasa ba.
Amaechi dai shine yazo na 2 a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2022 wanda Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaben.
Yace idan suka dage a matsayinsu na ‘yan Adawa zasu iya kwace mulki daga hannun Tinubu.