
A yayin da ake shirin yin karin kaso 5% akan farashin man fetur a matsayin haraji, hakan yasa ‘yan Najeriya suka fara tuna baya.
Me gabatarwa na gidan talabijin din Arise TV, Rufai Oseni ya wallafa a shafinsa cewa, a shekarar 2003 lokacin Shugaban kasa Bola Tinubu ya yana Gwamnan Legas, shugaban kasa a wancan lokacin, Olusegun Obasanjo ya so saka haraji kan man fetur.
Yace amma a wancan Lokacin sai Bola Ahmad Tinubu ya ki amincewq da hakan.
Inda yace gar zai kai kaa kotu.
Saidai gashi kuma shi zai kakabawa ‘yan Najeriya harajin kaso 5% nan da shekarar 2026.