
Wannan wani dan Najeriya ne da a shekarar 2020 ya sayi kayan abinci akan Naira 25,000.
Saidai a shekarar 2026 da muke ciki ya koma ya sake sayan kalar wadannan kayan abincin komai da komai saidai farashinsu ya karu zuwa Naira 147,000.
Hakan na nufin farashin kayan ya karu da kusan kaso 6 kenan.
Ya kuma wallafa rasit din abin a shafinsa na X.
Lamarin dai ya dauki hankula sosai inda akai ta tattauna yanda farashin kayan masarufi ke kara tashi.
