
A Wasu Lokutan Yawan Roko Ne Ke Hana Wasun Mu Shiga Cikin Jama’a Idan Mun Dawo Gida Yin Hutu Daga Turai, Cewar Dan Kwallon Nijeriya, Sadiq Umar Wanda Ke Wasa A Kungiyar Valancia Dake Kasar Sifaniya
Sadiq Zololo ya kara da cewa misali kamar shi ya yana son shiga cikin abokansa ko ‘yan uwansa a yi hira amma tun kafin a fara hira mutum zai soma gabatar maka da bukatunsa. Kuma idan ba ka bayar ba a yi fushi da kai.