
Masana sararin samaniya na kasar Amurka, NOAA sun bayyana cewa, akwai yiyuwar wani mulmule daga rana zai fado Duniyarmu a yau Lahadi.
Sun bayyana cewa, mulmulen na da sauri sosai inda yake gudun kisan Kilometres 1000 a duk sakan ko dakika.
Sun ce zuwansa Duniyar mu ka iya shafar wutar lantarki da yadda Intanet ke aiki.
Saidai basu bayyana a wane yanki ne zai fado ba.