
A yau, Litinin, Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar Filato dan jajantawa iyalan wadanda aka kashe a hare-haren da suka faru a jihar.
Mutane sama da 100 ne aka kashe a jihar biyo bayan wasu munanan hare-haren da aka kai a cikin makonnin nan.
Ministan jinkai da rage Talauci, Dr. Nentawe Yilwatda ne ya tabbatar da zuwan mataimakin shugaban kasar a yayin da ya kai ziyara Bassa ranar Asabar dan ganewa idansa yanda lamarin ya faru.
Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kansa ne ya baiwa Kashim Shettima umarnin kai wannan ziyara.
A yayin ziyarar tasa ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai gana da masu ruwa da tsaki na yankin dan samo hanyar magance wannan matsalar.