
A yau, Alhamis ne ake sa ran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sakawa sabbin kudirin dokokin Haraji hannu a fadarsa dake Abuja.
Hakan na kunshene cikin sanarwar da kakakin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar.
Kudirin dokokin guda 4 ne wanda tuni majalisar tarayya ta amince dasu bayan cece-kuce da suka jawo sosai.
Shuwagabannin majalisar tarayya da shuwagabannin kungiyoyin gwamnoni da ministan kudi da sauran manyan ma’aikatan Gwamnati ne zasu shaida wannan lamari a fadar shugaban kasar kamar yanda sanarwar ta tabbatar.