Wednesday, August 19
Shadow

A yau shugaba Tinubu zai sakawa sabbin dokokin Haraji hannu

A yau, Alhamis ne ake sa ran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sakawa sabbin kudirin dokokin Haraji hannu a fadarsa dake Abuja.

Hakan na kunshene cikin sanarwar da kakakin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar.

Kudirin dokokin guda 4 ne wanda tuni majalisar tarayya ta amince dasu bayan cece-kuce da suka jawo sosai.

Shuwagabannin majalisar tarayya da shuwagabannin kungiyoyin gwamnoni da ministan kudi da sauran manyan ma’aikatan Gwamnati ne zasu shaida wannan lamari a fadar shugaban kasar kamar yanda sanarwar ta tabbatar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon hira da matarnan da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta saboda mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *