Majalisar tattalin arzikin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana damuwa kan yanda farashin tumatur yayi tashin gwauron zabi.
Ta bayyana hakane yayin da farashin tumatur din ya tashi daga Naira dubu arba’in(40,000) zuwa Naira dubu dari da hamsin (150,000).
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.
Yace hauhawar farashin kayan masarufi na kara jefa mutane cikin wahala.