
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi gargadi cewa muddin ‘yan Najeriya basu tashi tsaye ba suka yi abinda ya kamata a 2027 ba, to lallai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai so ya zarce ya mulki Najeriya har iya tsawon rayuwarsa.
El-Rufai ya kwatanta Abinda Tinubu ke son yi da irin mulkin shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.
El-Rufai yayi wannan maganane a yayin da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai masa ziyarar jaje bayan tarwatsa taron ADC da aka yi a Kaduna.
El-Rufai yace ko mulkin Soja bai ga ana yin irin kamar karyar da Gwamnatin Tinubu ke yi ba
Dan haka yace dolene a hada kai.