Wednesday, January 15
Shadow

Alamomin cikin wata bakwai

A yayin da cikinki ya kai watanni 7, zaki iya fuskantar matsala saboda nauyin abinda ke cikinki.

Gwiwoyi da kafafuwanki zasu iya kumbura.

A wannan lokaci ne ya kamata ki samu ilimi kan haihuwa saboda kina kusa da haihuwar.

Canji a jikin uwa bayan da ciki ya kai wata bakwai:

Zaki iya samun matsalar rashin bacci.

Zaki iya samun matsalar zubewar gashi wanda bayan kin haihu zai dawo.

Zaki iya ganin karuwar gashi a fuska, gabanki, hamata, kafa da baya

Faratan ki zasu rika girma sosai.

A yayin da cikinki ya kai watanni 7 da haihuwa, zaki fuskanci fargaba saboda kin kusa haihuwa, zaki rika tunanin nakuda da rainon yaron.

Karanta Wannan  Basir ga mai ciki

Halartar wajan bitar abubuwan da zaki yi nan gaba wajan haihuwa da bayan haihuwa zai taimaka sosai.

Canje-Canjen da ake samu a jikin jariri yayin da ciki ya kai wata 7:

Nauyin cikin zai kai 1,600 g da kuma tsawonsa zai kai 40 cm.

Hankalo ya fara shigar jaririn a wannan lokaci, ya fara gane muryar mahaifiyarsa sannan idan ta yi magana zai ji ta.

A wannan lokaci, kwakwalwarsa na ci gaba da habaka ana gina bangaren basira na kwakwalwar tasa.

Huhu da sauran bangarorin jikin jaririn na ci gaba da habaka.

Abubuwan dake faruwa kenan yayin da ciki ya kai wata 7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *