A sati na 5 zuwa 6, abinda ke cikinki zai fara canjawa inda zai shiga matakin Embryo wanda daga wannan mataki ne za’a fara halitta.
Zai dunkule a waje daya wanda zai zama kamar zuciya amma bai gama zama zuciyar ba. Idan aka duba a ma’aunin Ultrasound za’a iya jin yana motsi kamar zuciya.
Alamun fitowar hannuwa da kafafu zai bayyana.
Halittar da Kwakwalwa, jijiyoyi da sauran manyan sassan jiki zasu fita daga ciki zata bayyana.
Alamar bindi zata bayyana.
Ya yin da cikin ya cika sati 8, watau wata biyu daidai, zuciya zata bayyana
Yatsun hannu da na kafa zasu fara bayyana.
Ido, kunne, marfin ido ko fatar ido zasu fara bayyana. Da leben sama.
A wata na biyu, har yanzu alamomin daukar ciki suna nan tare dake kamar su zafin nono, kasala, yawan fitsari, zafin kirji ko zuciya, rashin lafiya da safe, da amai duk za su yi ta karuwa.
Abubuwan dake faruwa kenan a wata na biyu bayan daukar ciki.