Ciwon zuciya na daya daga cikin abubuwan dake kashe mata da maza.
Alamomin ciwon zuciya kusa dayane ga duka mata da maza.
Ga alamomin ciwon zuciya ga mata kamar haka:
Ciwon wuya, haba, kafada, baya, da saman ciki.
Sarkewar Numfashi.
Jin ciwo a daya ko duka hannuwa.
Yawan ciwo da safe da amai.
Zufa.
Jin kanki ba nauyi da Juwa.
Jin Kasala sosai.
Zafin Zuciya.
Abubuwan da ka iya sa ciwon zuciya ya tsananta a jiki mata:
Ciwon Suga: Duk macen dake fama da ciwon sugar na cikin hadarin iya kamuwa da ciwon zuciya.
Damuwa da Kunci: Matsalar damuwa da kunci ta fi baiwa mata alamun kamuwa da cizon zuciya fiye da maza.
Shan Taba ko Wiwi:Mace me shan taba ko wiwi tafi maza zama cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya fiye da maza.
Rashin Motsa jiki: Yawan zama ba tare da yin wani abu na motsa jiki ba na taimakawa matuka wajan kamuwa da cutar zuciya.
A yayin da mace ta daina Haihuwa tana cikin hadarin kamuwa da cutar zuciya.
Laulayin ciki: Laulayin ciki da matsalolin dake tattare dashi na iya jefa mace cikin halin kamuwa da ciwon zuciya.
Idan danginku na da tarihin yin fama da ciwon zuciya: Wannan matsala ta fi shafar mata akan maza.
Matan dake kasa da shekaru 65 wanda danginsu akwai masu fama da ciwon zuciya sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar.
Yawan motsa jiki ko da na minti 30 ne ko ma mintuna 5 a rana yana taimakawa lafiyar zuciya, hakanan cin abinci me gina jiki. A daina shan giya, taba da sauransu, a yi kokarin kaucewa shiga damuwa.