
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, Albashin Naira 100,000 da kuma kudin abinci na Naira 5,000 da ake baiwa sojoji kullun yayi kadan.
Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai inda yace hakan ba zai karfafa sojoji su gudanar da ayyukansu yanda ya kamata ba.
Sanata Ali Ndume na martanine kan wasu dake kiran a sauke shuwagabannin sojojin.
Yace matsalar ta karancin kudi ce.