Wednesday, March 4
Shadow

Allah Sarki: Kalli Bidiyon wa’azin da ya saka aka dakatar da Sheikh Alkali Zaria

Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar Izala ta dakatar da Sheikh Alkali Zaria saboda wani wa’azi da yayi.

Ga wasu daga cikin dalilan da suka sa aka dakata dashi kamar haka;

TIRƘASHI: Ga Dalilin Dakatarwar Sheikh Alƙali Zaria Daga Gudanar Da Tafsirin Ramadan A Damaturu

Daga Shafin JIBWIS Jos, Reshen Damaturu

Dakatarwar ta samo asali ne daga wasu jawabai da Sheikh ɗin ya yi a lokuta daban-daban kamar haka:

  • Khutba da nasiha da ya gabatar a Hedkwatar ‘Yan Sanda ta Jihar Yobe a ranar Juma’ar da ta gabata.
  • Nasiha da ya yi da asuba a Masallacin Alimarami, ranar Asabar.
  • Tafsirin da ya yi da daddare a Masallacin Mokas ranar Juma’a, inda aka ce ya bayyana wasu kalamai sanye da kayan agaji.
  • Wadannan abubuwa, a cewar majalisar, sun shafi jama’a da dama ciki har da jami’an tsaro, gwamnoni, har ma da shugaban ƙasa.
Karanta Wannan  Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na shirin komawa jam'iyyar ADC

An bayyana cewa irin salon da Malam ya yi amfani da shi na ambaton sunayen mutane da tsinuwa da ja fa’i, ya saba wa ƙa’idojin koyarwar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Iqamatissunnah (JIBWIS).

A ranar 14 ga Ramadan 1447, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya kira Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria, tare da Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Yobe, da kuma wakilan Ƙaramar Hukumar Damaturu (mutum uku).

A taron, Sheikh Alkali ya gabatar da jawabinsa, sannan kowa ya yi nasa bayani. Daga ƙarshe, an cimma matsaya cewa ci gaba da tafsirinsa a Damaturu ba zai kasance da alkhairi ba, saboda haka aka janye posting ɗinsa daga Damaturu.

Karanta Wannan  Mun Baka Wata 6 idan baka tabuka abin azo a gani ba, zamu sa a tsigeka>>Majalisar Tarayya ta gayawa Janar Christopher Musa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *