
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL sun sanar da kammala hada bututun iskar gas na AkK wanda aiki ne da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fara.
Shiri ne wanda zai kai Iskar Gas zuwa masana’antun Arewa musamman wadanda ke Ajakuta, da Kano da Kaduna.
Shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Ojulari ne ya bayyana hakan bayan ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Yace ya je gurin shugaba Tinubu ne dan sanar dashi irin ci gaban da suka samu a shekarar 2025.
Yace yanzu zasu iya hada masana’antun arewa masu bukatar gas da gas din ta hanyar amfani da wadannan bututun da aka kammala hadawa.