Wednesday, January 15
Shadow

Amfanin lemun tsami ga mace

Lemun tsami (lemon) na da amfani mai yawa ga mace.

Ga wasu daga cikin amfanin sa:

  1. Inganta lafiyar fata: Lemun tsami na dauke da Vitamin C, wanda yake taimakawa wajen kawar da kuraje, sassauta fata, da kuma gyara lalacewar fata sakamakon dadewa a rana inda zaka ga fuskar mutum ta yi duhu.
  2. Kwari: Zaki iya amfani da lemon tsami wajen rage kiba da taimakawa wajen narkar da abinci. Yana taimakawa wajen rage kitsen jiki da kuma narkar da abinci yadda ya kamata.
  3. Ciwon mara na al’ada: Lemun tsami na taimakawa wajen rage radadin ciwon mara na al’ada saboda yana dauke da wasu sinadaran dake rage kumburi da kuma ciwon, ana hada lemun tsami da citta a sa a ruwan dumi ko a tafasasu a bari ruwan ya huce a sha lokacin jinin al’ada dan maganin ciwon ciki.
  4. Karfafa garkuwar jiki: Vitamin C da ke cikin lemun tsami yana karfafa garkuwar jiki, wanda zai taimaka wajen guje wa kamuwa da cututtuka.
  5. Kare gashi: Lemun tsami na taimakawa wajen rage faduwar gashi da kuma bunkasa saurin tsawon gashi.
  6. Kula da baki: Lemun tsami na taimakawa wajen kawar da warin jiki da kuma gyaran hakora.
  7. Lemun Tsami na taimakawa zuciyar mata wajan aiki yanda ya kamata da kuma kareta daga ciwo da kariya daga cutar shanyewar rabin jiki.
  8. Akwai binciken masana da yawa da suka tabbatar da lemun tsami yana kashe kwayoyin cutar cancer ko cutar daji.
  9. Lemun tsami yana kashe kurajen fuska yana kuma kashe amosani dake sa kai yayi fari yana zubar da gari ko kuma yana yawan kaikai.
Karanta Wannan  Illolin lemon tsami

Zaki iya amfani da lemon tsami ta hanyoyi da dama, misali, shan ruwan lemon tsami da ruwa mai dumi da safe, amfani da lemon tsami a abinci, ko shafawa a fata da gashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *