Macen da gabanta bashi da ruwa ko baya kawo ruwa, yana bushewa, musamman a lokacin jima’i tana iya amfani da man kwakwa.
Man kwakwa inji masaana yana hana bushewar gaban mace.
Hakanan a wani kaulin, Man kwakwa yana sa hasken gaban mace. Ana shafashi shi kadai, ko kuma domin samun sakamako me kyau, a hada da ruwan lemun tsami a shafa, yana sa gaban mace yayi haske.
Hakanan man kwakwa yana maganin kaikayin gaba dake damun mata ko kuma ace infection. Ana shafa man kwakwa a gaba dan magance yawan kaikai dake sa susa a ko da yaushe.
Ana iya shafashi a saman gaban mace ko kuma a shafashi a cikin gaban, duk yana magani.
Hakanan bincike ya nuna cewa,Man kwakwa na taimakawa mata masu fama da matsalar yoyon fitsari.