Monday, December 16
Shadow

Amfanin man kwakwa a nono

Bincike ya tabbatar da man Kwa na maganin bushewa ko tsagewar kan nono.

Ana shafa man kwakwa akan nono da yake bushewa ko ya tsage dan dawo dashi daidai.

Hakanan idan kan nono yana zafi ko yana ciwo,shima bincike ya tabbatar da cewa, ana shafa man kwakwa kuma ana samun sauki da yardar Allah.

Kuma idan kan nono yana kaikai, shima ana shafa man kwakwa dan magance wannan matsala.

Hakanan wasu bayanai sun ce shafa man kwakwa akan nono yana batar da nankarwa da karawa nonon lafiya.

Hakanan wasu bayanai sunce ana amfani da man kwakwa wajan sanya kan nono yayi haske, saidai bayanin yace sai an dauki lokaci kamar wata 2 ana shafawa kamin a samu sakamako me kyau.

Karanta Wannan  Gyaran nono su tsaya

Hakanan wasu bayanai da ba’a tabbatar dasu ba sun ce shafa man kwakwa yana tayar da nonuwan da suka zube. Ana iya gwadawa a gani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *