Thursday, October 3
Shadow

Gyaran nono da man kadanya

Wasu bayanai sun nuna cewa man kadanya yana sanya nonon mace ya kara cikowa kuma ya mike sosai ko ya tashi tsayen, haka kuma a wani kaulin yana maida tsohuwa yarinya.

Watau yana hana fatar nonon tsufa da wuri.

Akwai hanyoyi biyu da wasu bayanai na gargajiya sukace ana amfani dasu wajan gyaran nono da man kadanya.

Na farko shine, ana hadashi da man wanke baki watau Makilin a shafa akan nono zuwa wani lokaci a wanke.

A bayani na biyu kuma, an samo cewa ana samun man kadanya ko man kade shi kadai a rika shafashi akan nono a hankali kamar ana mai tausa.

Saidai duka wadannan bayanai basu da inganci a wajan likitoci, hanyoyi ne na gargajiya na gyaran nono a gida.

Karanta Wannan  Amfanin rigar nono ga budurwa

Abinda ya tabbata shine, idan nononki na kaikayi, zaki iya shafa man kade, yana maganin kaikayin nono da kaikayin kan nono.

Hakanan idan nonon yana bushewa sosai musamman lokacin sanyi har ya rika tsagewa, shima ana iya amfani da man kade.

Idan nono yana kumburi wanda bai dade ba shima ana iya gwada shafa man kade. Amma idan ba’a samu sauki ba bayan kwana biyu a gaggauta zuwa Asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *