Wednesday, January 15
Shadow

Amfanin toka a hammata

Toka na da amfani sosai wajan gyara hammata da hanata wari.

Ana amfani da Toka da Lemun tsami wajan tsaftace hammata dan hanata wari da zufa kuma wannan dabarace da aka yi amfani da ita shekaru aru-aru da suka gabata.

Ga yanda ake yi kamar haka:

Ana samun lemun tsami.

Sannan a samu Toka ta itace ko gawayi.

A tace tokar sannan a matse lemun tsamin a cikinta, a kwaba, sannan a shafa a hamatar.

A bari yayi kamar minti biyar sannan a wanke. Ana iya yin hakan sau 2 a sati.

Saidai idan bai karbi fatar ki ba a dakata amfani dashi, misali idan yana sanya yawan kaikai a hamatar ko yana kawo kuraje.

Sai a daina a yi amfami da sauran dabarun tsaftace hamata na kasa:

YADDA ZA A TSAFTACE HAMMATA

Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin namu na kwalliya.

A yau na kawo muku yadda ake da hammata.

Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda ya fi muhimmanci da a kula da shi.

Musamman ma bayan an aske gashin gurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin baki.

Ababe da dama ne suke kawo hammata ta yi baki koda an aske gashin gurin. Yawan zufa da amfani da man cire gashi gashin hammata da yawan kiba da kuma amfani da turare masu karfi a hammata.

Karanta Wannan  Yadda ake hada maganin infection

GA HANYOYIN KAMAR HAKA

AMFANI DA MAN KWA-KWA:
Babban abin da ake amfani da shi a wajen hada man zamani shi ne man kwa-kwa domin yana dauke ne da sinadarin kara haske kuma yana da vitamin E.


A shafa man kwa-kwa a hammata a kullum a yi minti goma kafin a yi wanka. Bayan an yi haka, sai a wanke da sabulu mara karfi (wanda sinadaran da akan hada shi ba mai zafi ba ne) da ruwan dumi.

*AMFANI DA GURJI DA LEMON TSAMI:
Kamar yadda aka sani cewa ruwan lemon tsami na dada hasken fata, haka kuma gurji shi ma na dauke da sinadarin kara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulbi. A hada ruwan lemon tsami da markadaddiyar gurji a guri daya sannan a shafa a hammata. A bari ya jima na tsawon mintuna goma sannan a wanke da ruwan dumi.

*GARIN KURKUM DA KWAI:
Kurkum ma na dada wa fata haske, za a iya kwaba garin garin kurkum da ruwan kwai sannan a shafa a hammata bayan mintuna goma zuwa sha biyar sai a wanke da ruwan dumi. A kullum kafin a yi wanka.
Aski; a daina barin hammata da gashi a yi kokarin aske shi a lokacin da ya fito. Domin idan da akwai gashi a hammata, zai hana gumi bushewa zai fara tara shi yayi ta ba da wani irin wari. Sai a ga koda an fesa turare, sai a ji kamshin turaren daban, warin hammata kuma daban.
Yin amfani da wadannan ababen wajen gyaran hammata zai rage warin jiki da kuma hana fesowar kuraje da fitowar bakar kala a karkashin hammata da kuma rage gumin hammata.

Karanta Wannan  Alamomin ciwon ulcer

HANYOYI GOMA (10) WANDA ZA A BI DON GYARAN JIKI

Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan fili namu na kwalliya. A yau na kawo muku hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba. Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa maigida. Idan maigida ya saba ba da kudin sayan kayan kwalliya, ranar da babu kuma sai a hakura a gwada daya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki. A sha karatu lafiya.

1⃣- Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da kwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar (15) zuwa talatin (30) sannan a wanke.

2⃣- Domin gyara farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar (5) sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi matukar kyau sosai.

3⃣- Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa ashirin (20) sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya ma a sati za a ga canji.

Karanta Wannan  Maganin daina shan taba

4⃣- Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke makale a gefen gashin kai.

5⃣- Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.

5⃣- Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rika dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.

6⃣- Man kwa-kwa na matukar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.

7⃣- Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.

8⃣- A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai. Sannan a rika shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai.

9⃣- Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *