Tuesday, June 30
Shadow

Aminu Warkal ya bayyana dalilin da yasa ya hana matarsa daukar magungunan da aka bata a asibiti bayan ya saketa duk da tana dauke da ciki

Aminu Warkal ya bayyana cewa, dalilin da yasa ya hana matarsa daukar magungunanta na Asibiti duk da tana dauke da ciki bayan ya saketa, shine sata ta masa.

Matar Aminu dai ta zargeshi da cewa ya hanata daukar maganin ta da aka bata a asibiti bayan ya saketa.

A martaninsa, yace dalilinsa shine, matar tasa sata tai masa, ta dauki dabbobinsa ta sayar, kuma yace ta dawo masa da dabbobinsa amma taki, sannan babu magana me dadi, shiyasa shi kuma yace ko allura ba zata dauka ba daga gidan.

Saidai Aminu Warkal yace duk da wannan, da zata fito ta bashi hakuri, shikenan maganar zata wuce.

Karanta Wannan  ABIN ALFAHARI: Matasa Uku Daga Jihar Gombe Sun Kammala Karatun Jami'a A Garin Madina Dake Kasar Saudiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *