
Dan fafutuka, IG Wala ya bayyana cewa, Zai jagoranci wata zanga-zanga wadda za’a tabbatar da cewa kowane dan majalisar tarayya an koreshi daga gidansa ya koma majalisa da zama.
Yace zasu bi duka gidajen ‘yan majalisar tarayya su tabbatar cewa an koresu sun koma majalisar da zama.
Yace abinda ake so su yi shine su tursasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya magance matsalar tsaro ko kuma idan ba zai iya ba, su tsigeshi.
Yace ba ana maganar dan kishin kasa ba, yace duk wanda yake son ya rayu zuwa gobe shine ake so ya fito a yi wannan zanga-zangar dashi dan matsalar tsaro ta ta’azzara.