Monday, December 16
Shadow

Amurka ta fara janye sojojinta daga jamhuriyar Nijar

Sojojin Amurka sun fara janyewa daga Nijar kamar yadda tashar talabijin ta ƙasar, Tele Sahel ta rawaito.

A wani biki da aka yi a Air Base 101 da ke birnin Yamai, babban hafsan sojojin Nijar, Kanal Maj Mamane Kiaou, ya sanar da cewa, sojojin Amurka 260 daga cikin kiyasin 1,100 da aka kiyasta sun janye daga ƙasar tare da tankunan kayan aiki da dama.

Maj Kiaou ya bayar da tabbacin cewa Nijar za ta tabbatar da tsaron jami’an Amurka a lokacin janyewar da ake sa ran kammalawa a tsakiyar watan Satumba.

Duk da janyewar, ƙasashen biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a ranar 8 ga watan Yuni, inda suka tabbatar da cewa dangantakarsu ba za ta ɓaci ba.

Karanta Wannan  Darajar Naira ta fadi a kasuwar Canji

Janyewar sojojin ta biyo bayan sanarwar da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bayar a ranar 16 ga watan Maris, inda ta soke yarjejeniyar da ta bai wa sojojin Amurka damar gudanar da aiki a kasar nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *