Wednesday, January 15
Shadow

An ba ni minista ne domin APC ta ƙwato Kano – Yusuf Ata

Sabon ƙaramin ministan ƙasa na gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya ce ƙudurinsa shi ne jam’iyyar APC ta ƙwato jihar Kano a 2027.

Ata ya bayyana hakan ne bayan da ya koma Kano bayan da aka rantsar da shi a matsayin ɗan majalisar zartarawa ta gwamnatin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, Ata ya bayyana cewa : “An nada ni muƙamin ne saboda siyasa kawai, APC ta rasa jihar Kano yanzu kuma za ta ƙwato ta. Babbar matsalar daga Kano ta Tsakiya take kuma daga nan nake.

“Duk da matsayina na minista zan ci gaba da zama a wannan mazaɓa, za mu yi aiki tuƙuru domin ganin APC ta ci jihar Kano a 2027.,” in ji Ata.

Karanta Wannan  ‘Yan Bindiga sun kashe mutane 7 da sace 150 a Munya jihar Naija saidai an kashe ‘yan Bindigar guda 25

Ƙaramin ministan ya bayar da tabbaci ga Shugaba Tinubu cewa a 2027, jihar Kano za ta kasance ta APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *