Friday, December 5
Shadow

An daure magidanci daurin rai da rai bayan da yawa diyar makwaucinsa me shekaru 8 fyàdè

Wani me aikin gini me suna Azeez Shoderu wanda aka fi sani da Chisco ya gamu da daurin rai da rai bayan da aka kamashi yama yiwa diyar makwaucinsa me shekaru 8 fyade a bandaki.

Kotu ta musamman dake jihar Legas wadda aka samar domin hukunta irin wadannan laifuka ce ta yanke masa wannan hukunci.

Mai shari’a, Rahman Oshodi ce ta yanke masa wannan hukunci bayan samunsa da laifi bisa dogaro da shaidu da hujjoji.

Wanda ake zargin dai ya ki amsa laifinsa inda yace kawai yace yarinyar ta kawo masa ruwane a bandakinsa.

Saidai Yarinyar tace ta shiga bandaki dan yin fitsarine sai ya kamata ya rufe mata baki ya mata fyade.

Karanta Wannan  Zan Shiga gaba wajan Nemawa Nnamdy Khanu Afuwa a wajan Gwamnati idan ya nuna Nadama>>Inji Sheikh Gumi

Kotu tace ta gamsu da maganar yarinyar musamman bayan da binciken likitoci ya tabbatar da an mata fyade.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *