Wednesday, January 15
Shadow

An kama Alkali da zargin satar kudi a asusun me laifi da aka kai kotu ake tuhumarsa a Kano

Hukumar kula da Shari’a ta Kano ta hukunta wasu alkalai a jihar saboda aikata ba daidai ba.

Alkalai uku ne dai da maga takarda a babban kotun jihar aka hukunta ciki hadda alkalin da yayi yunkurin satar kudi daga asusun wanda ake tuhuma.

Kakakin hukumar Baba Jibo-Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Yace wadanda ake zargin sune Magistrate Rabi Abdulkadir, Magistrate Talatu Makama, da Magistrate Tijjani Saleh-Minjibir.

Sanarwar tace an dauki matakin ladabtarwar ne dan tsaftace bangaren shari’a na jihar.

Karanta Wannan  Hotuna: YANZU-YANZU Zanga-Zanga Ta Barke A Masarautar Rano Dake Kano Kan Rikicin Sarauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *