
Wata malamar makaranta a garin Rochdale Shawnee Nicole Despain me shekaru 26 na fuskantar tuhuma bayan da aka sameta da laifin yiwa dalibinta me shekaru 17 fyade.
Malamar na karantarwa ne a makarantar Rockdale High School dake jihar Texas ta kasar Amurka. Da farko dai ta musanta zargin.

Saidai daga baya an gano sakonnin soyayyar da suka rika aikawa juna ita da dalibin nata hadda ma hotunansa tsirara a wayarta.
Sannan ta boyewa mijinta bata gaya mai cewa cikin da take dauke dashi ba nashi bane na dalibinta ne sai da aka yi bincike aka gano hakan.
Malamar dai zata iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari amma a yayin yanke hukunci, Alkali ya yanke mata hukuncin daurin talala na shekaru 10 sannan an kwace lasisinta na aikin koyarwa.