
‘Yansanda a jihar Borno sun sanar da kama mutane 2 bisa zargin kisan da sukawa wata mata me shekaru 70 a Biu dake jihar bayan zarginta da maita.
Kakakin ‘yansandan jihar, CP Yusuf Lawan ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ranar Asabar, 22 ga watan Fabrairu 2025.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargi kamar haka,Ja’o Muhammad, Idrisa Muhammad, 20, da Ya’u Muhammad, 30.
Yace matar sunanta Hajara Saleh wadda aka kashe a Bantine dake Biu.
Hukumar ‘yansandan tace mutanen da ake zargin sun hada kai dan kashe Hajara inda suka zargeta da maita da jawowa garinsu bala’i.
Ya bayar da tabbacin hukunta wadanda ake zargin.