Jami’an ‘yansanda a jihar Gombe sun kama wani karamin yaro dan shekaru 13 saboda yiwa yarinya me shekaru 8 fyade.
Ya aikata laifinne a karamar hukumar Akko dake jihar ta Gombe.
Hakanan an kama wani Usman Husseini dan shekaru 18 da kuma wani Mohammed Yaya shi kuma dan shekaru 45 da duka ake zargi da yin fyade a jihar.
Kakakin ‘yansandan jihar, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace yaron ya ja yarinyar zuwa wata hanya da ba kowa inda acanne ya zakke mata.
Shi kuma Mohammed Yahya yawa yarinya me shekaru 10 fyadene a lokuta daban-daban inda wani lokacin yake bata Naira 100 wani lokacin kuma ya bata Naira 50.
Shima ya fito ne daga Tumu karamar hukumar Akko.
Yace ana bincike akan lamuran kuma za’a gurfanar da wadanda ake zargi a Kotu.