
Allah Sarki
Wannan wata ‘yar Kasuwace da take bayani tana kuka.
Tace wani ya je shagonta yayi sayayyar Naira dubu dari biyu da hamsin yayi transfer bata nan, sai yarinyar shagonta ta kirata ta gaya mata.
Tace sai ta cewa yarinyar kada ta bari mutumin ya tafi ya jira ta tabbatar kudin sun shiga.
Tace amma sai da yarinyar ta bar mutumin ya tafi kuma bata ga kudin ba a asusunta.