
Rahotanni daga jihar Benue na cewa, an rushe sabon ofishin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da aka gina a jihar.
Ranar Alhamis ne Hukumar kula da raya birane ta jihar Benue din ta rushe wannan gini wanda kuma shine Hedikwatar yakin neman zaben Tinubu a jihar.
Sati daya kenan da bude wannan ofishin.
Shugaban kungiyar magoya bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jihar Tarnongo Simon yayi Allah wadai da lamarin inda yace sun cika duka sharudan mallaka da ginin wannan ofishi nasu kamin a rusheshi.