Friday, December 5
Shadow

An saka ranar da shugaba Tinubu zai mayar da gwamban Rivers, Simi Fubara kan kujerarsa ta Gwamna

Rahotanni na cewa, a watan Yuli ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai mayar da gwamnan Rivers, Simi Fubara kan mukaminsa.

Hakanan itama majalisar jihar a wannan watanne ke tsammanin mayar da ita kan aiki.

Hakan na zuwane bayan da aka yi sasanci tsakanin Fubara da Wike.

A ranar 18 ga watan Maris ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara da ‘yan majalisar jihar inda ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri musamman game da fasa bututun man fetur a jihar kuma Gwamnan ya kasa magance matsalar.

Karanta Wannan  Sojoji sun ce sun lalata sansanin Bello Tùrjì tare da kkashe 'yànbìndìgà 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *