Thursday, February 5
Shadow

An tashi baram-baram a zaman sulhu da aka yi yunkurin yi tsakanin kungiyar PENGASSAN da Dangote

Rahotanni sun ce zaman sulhu da aka yi tsakanin wakilan kungiyar PENGASSAN da na Matatar Dangote an tashi ba tare da cimma matsaya ba.

Gwamnatin tarayya ce ta kira zaman wanda aka fara ranar Litinin da misalin karfe 4 p.m..

Ministan kwadago, Mohammed Dingyadi da karamar ministan Kwadago, Nkiruka Onyejeocha sun halarci zaman wanda aka shafe awanni 9 ana yi.

Minista Dingyadi yace za’a dawo ci gaba da zaman da misalin karfe 2 p.m. na ranar Talata.

Gwamnatin tarayya tace tana duba abinda wannan rikici zai jawowa Najeriya ne shiyasa take kokarin sulhunta Bangarorin Dangote da PENGASSAN.

Karanta Wannan  Na yi nadamar yiwa Tinubu yakin neman zabe, Jama'a ku yafe min kan jawo hankalinku da na yi kuka zabeshi>>Dan Balki Kwamanda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *