Thursday, May 8
Shadow

An yankewa matashi hukuncin kìsà saboda kàshè Kishiyar mahaifiyarsa me dauke da juna biyu da diyarta a Kano

Babbar kotu a jihar Kano ta yankewa matashi me suna Sagir Rijiyar-Zaki dan kimanin shekaru 22 hukuncin kisa bayan samunsa da laifin kashe kishiyar mahaifiyarsa da diyarta.

Sagir ya yi amfani da sukundireba ya cakawa kishiyar mahaifiyarsa me suna Rabiatu Sagir me kimanin shekaru 25 sannan ya shage diyarta, Munawwara me shekaru 8 itama ta mutu.

A ranar April 22, 2025 ne Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ya ce an gabatar da gamsassun shaidu da suka tabbatar wanda ake zargi yayi kisan.

Dan haka ya yankewa wanda ake zargin hukuncin kisa ta hanyar Rataya.

Karanta Wannan  Darajar Naira ta fadi a kasuwar Chanji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *