Rahotanni daga ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun ce an yi jana’izar ‘yan aikin sa kai da wani jirgin yaƙi da ake zargin na sojojiin Najeriya ya kai musu hari bisa kuskure a ƙauyen Tungar Kara.
Wani mazaunin ƙuyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tuni aka yi jana’aizar ‘yan sa kan su 17 da suka mutu a harin, yayin da wasu ke kwance a asibiti.
A ranar Asabar da maraice ne wani jirgi da ake kyautata zaton na sojin ƙasar ne ya kai hari bisa kuskure kan ‘yan sa kai a ƙauyen na Tungar Kara.
Lamarin ya auku ne, yayin da suke ƙoƙarin daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai garin, suna ƙoƙarin kore wasu dabbobi.
Wani mutum – da ya rasa ɗan’uwansa a harin, ya bayyana wa BBC cewa ƴan sa kai da dama ne lamarin ya rutsa da su yayin da suke yunƙurin tunkarar ƴan bindigan da aka ce suna ɓarna a yankin, inda ya kara da cewa ƴan bingidan sun riga sun bar yankin a lokacin da jirgin ya fara ɓarin wuta..
Ya ce: ”Muna zaune sai muka ga jirgi ya nufi wuraren da aka ce ƴan bindigan suke, amma ko a lokacin sun riga wuce. Waɗannan yaran da mutanen da ke ƙasa ne wannan jirgin yake ta harbi, yanzu haka ga ɗan yaya na an kawo mun shi a mace.”
Jami’in watsa labarai na rundunar operation Fansar Yamma da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, inda ya ce zai bincika ya tuntuɓe mu. Haka shi ma mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya shaida mana.
To sai dai wata majiyar gwamnatin jihar, wanda ta buƙaci a sakaya sunanta, ya tabbatar wa BBC aukuwar wannan lamari, amma bai yi wani cikakken bayani ba.