
Wasu masu garkuwa da mutane dauke da makamai sun kai farmaki unguwar Grow Homes da ke cikin yankin Chikakore na Kubwa – wacce ita ce mafi girma cikin unguwannin da ke wajen birnin Abuja – da safiyar Litinin, inda suka yi garkuwa da mazauna unguwar.
Jaridar Vanguard ta rawaito daga bakin wasu mazauna unguwar da abin ya firgita cewa lamarin ya faru tsakanin karfe 12 na dare zuwa karfe 1:30 na dare.
Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da ganin wani namiji da wata mace suna cikin wadanda aka sace, ya ce da safiya an sami matar a cikin unguwar, bayan da masu garkuwar suka sako ta ba tare da bayani ba.
Sai dai bai tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.
“Lamarin ya faru kusan karfe 12 na dare. Wadannan mutane sun zo da makamai sosai, sun kuma fi karfin kungiyar tsaron sa-kai. ‘Yan sanda sun iso wajen misalin karfe 1 na dare, inda aka sha musayar wuta na tsawon kusan minti 30.
“Muna rokon gwamnati ta gyara wannan hanya don saukaka zirga-zirgar motocin tsaro. Haka kuma muna rokon ‘yan sanda da kuma hukumar gudanarwar FCT su taimaka su kafa ofishin ‘yan sanda a nan don samun saurin daukar mataki,” in ji shi.